Fankiris - Pancreas

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Fankiris



Siffar Fankiris   Hoto: Pancreapedia


Gabatarwa

Fankiris, wato Pancreas kenan a Turance, wani dogon sashen jiki ce mai ɗan faɗi wadda ke maƙale ta baya daga saman tumbi (Medline Plus, 2021; Cleveland Clinic, 2021), tana da tsawon da ya kai kimanin inci 6 (Jewel, 2018), ɗaya ce daga cikin sassan narkar da abinci (Cleveland Clinic, 2021). Wannan sashen jiki yana ɗauke da ƙwayoyin halitta biyu mabambanta da ke bashi damar yin ayyuka biyu mabambanta; samar da ƙwayoyin halittar da ke narkar da abinci wato enzymes kenan, da kuma beta sel (link), wato beta cells waɗanda su kuma alhakin samar da sinadarin insulin ya rataya a wuyansu.

Yadda Fankirisi Ke Aiki

Fankirisi tana ayyuka biyu a jikin ɗan'adam, farfasa abinci da kuma samar da sinadarin insulin. Kowane guda daga cikin waɗannan mabambantan ayyuka biyu na fankiris, akwai wasu ƙwayoyin halitta da suka keɓanta da shi da kuma yadda suke yin sa.


Siffar Fankiris   Hoto: Colorado University

Narkar da Abinci

Ta fuskacin narkar da abinci, fankiris tana samar da wasu ƙwayoyin halitta masu suna enzymes na'uka uku:

  1. Lifasi Lipase, wadda ruwan sinadari ne da ke aiki tare da wani ruwan sinadarin shima mai ɗaci wadda ke fitowa daga ƙoda (liver) da suke haɗuwa su ratattaka maiƙo.
  2. Amiles Amylase, wadda shi kuma alhakin ratattaka sinadarin kabohaidiret ya hau kansa.
  3. Furotis, shi kuma shi ne yake ratattaka sinadarin furotin.

Da zarar abinci ya samu shiga cikin tumbi (stomach), fankiris za ta saki waɗancan ƙwayoyin halitta bisa dacewa da nau'in abinci ta tura sinadarin zuwa cikin ƙaramin kwaroron da ya shiga babban kwaroronta. Shi kuma wannan babban kwaroro ya haɗu da kwaroron ƙoda, wadda ke da alhakin kai ruwan sinadarin can mai ɗaci zuwa cikin maɗaciya (gallbladder). Daga nan kuma sai ruwan sinadarin mai ɗaci ya tafi zuwa wani sashe na ƙaramin hanji wadda ake kira dudinom duodenum a Turance. Daga ƙarshe wannan ruwan sinadari na maɗaciya wato bile, za su haɗu da ƙwayoyin halittar can da fankiris ta saki wato enzymes su shiga cikin ƙaramin hanjin can su narkar da abincin.


Fankiris Haɗe da Hanji   Hoto: Pancreapedia

Daidaita Sukarin Jini

Wani sashe na fankirisi mai suna indokirin endocrine glands ne yake sakin wasu sinadarai da ake kira homons hormones waɗanda alhakin sarrafa sukarin cikin jini ya rataya a wuyansu waɗanda kuma su ne insulin da kuma gulucagon Glucagon.

Sassan Fankiris

Fankiri tana da sassa huɗu kamar haka:

  1. Kai (Head): Sashen fankiris mafi faɗi wadda ke zaune a kwalogon ƙaramin hanji.
  2. Wuya (Neck): Sashen Fankiris mafi gajarta wanda ya fara daga kai.
  3. Jiki (Body): Sashen da ke tsakanin kai da wuyan fankiris.
  4. Jela (Tail): Sashen fankiris mafi siririnta, wadda ke daf da sifilin spleen.


Siffar Fankiris   Hoto: Pancreapedia

Matsaloli

Idan fankiris ta samu matsala, to jiki kan samu cututtukan da suka haɗa da:

  1. Ciwon sukari nau'in farko: Wannan kan faru idan fankiris ta daina samar da insulin.
  2. Ciwon sikari nau'i na biyu: Wannan kan faru idan fankiris tana samar da insulin amma jiki baya amfani da shi yadda ya dace.
  3. Yawaitar sinadarin sukarin jini (Hyperglycemia): Yakan afku idan glucagon ya yawaita a jiki.
  4. Ƙarancin sinadarin sukarin jini (Hypoglycemia): Yakan afku idan sinadarin insulin ya yawaita a jiki.
  5. Fankiriyatitis (Pancreatitis): Yakan afku idan ƙwayoyin halittar enzymes suka fara aiki kafin shigarsu cikin ƙaramin hanjin, wadda kan haddasa ciwon tsakuwa, gallstone ko kuma yawaitar sinadarin giya alcohol. Wannan kuma ka iya zama na dogon lokaci ko kuma na ɗan lokaci ƙanƙani.
  6. Kansar Fankiri (Pancreatic cancer): Cuta ce da ƙwayoyin halitta masu suna Cancerous cells ke haifarwa, wadda kuma ke da wahalar ganowa da kuma magani.

Manazarta:

Cleveland Clinic (2021). Pancreas An ciro a 2021, daga https://my.clevelandclinic.org/health/body/21743-pancreas

Jewell T. (2018). What Does the Pancreas Do? An ciro a 2021, daga https://www.healthline.com/health/what-does-the-pancreas-do

Johns Hopkins university (2021). Pancreas Function. Department of Pathology, James Hopkins University, Baltimore, Maryland, USA.

Medline Plus (2021). Pancreatic Diseases. An ciro a 2021, daga https://medlineplus.gov/pancreaticdiseases.html

The National Pancreas Foundation (2021). Common Disorders of The Pancreas. An ciro a 2021, daga https://pancreasfoundation.org/patient-information/about-the-pancreas/common-disorders-of-the-pancreas/

Utter P. S. da Jacob D. (2020). What Is the Function of the Pancreas in the Body? An ciro a 2021, daga https://www.medicinenet.com/what_is_the_function_of_the_pancreas_in_

the_body/article.htm

 


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub